A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, littafin "Muhawarori 101 Masu Kayatarwa" wanda Muhammad Mohammadi Eshtehardi ya rubuta, ya tattara muhawarori daban-daban kan al'amuran akida da addini, wanda shafin Hawza News yake wallafa su daki-daki.
Muhawarar Ali bin Maytham Mai Karfi da Mai Musun Samuwar Allah
Wata rana Ali bin Isma'il (Ali bin Maytham) ya shiga wajen Hasan bin Sahl (Ministan Ma'amun). Ya ga wani mutum mai akidar "Dabi'a" (mai musunta samuwar Allah) yana zaune a babban matsayi a taron, kuma ministan yana girmama shi sosai, yayin da manyan mutane da masana suke zaune a matsayi na kasa da shi. Shi kuma wannan mutumin yana ta magana cikin rashin kunya game da gaskiyar akidarsa.
Ali bin Maytham ya ji ransa ya baci, sai ya fara muhawararsa kamar haka; ya ce wa Hasan bin Sahl: "Ya kai Minista, yau na ga wani abun mamaki kwarai a wajen gidan nan naka!"
Minista: "Me ka gani?"
Ali bin Maytham: "Na ga wani jirgin ruwa ba tare da matuki (direba) ko igiyoyi ba, yana tafiya da kansa daga wannan gaba zuwa wancan gaba!"
Nan take wannan mai musun samuwar Allah da ke zaune a wajen, ya ce wa Minista: "Shin wannan mutumin mahaukaci ne? Domin yana fadar maganganun da ba su da ma'ana."
Ali bin Maytham: "A'a, magana ta gaskiya nake yi, me ya sa ka ce ni mahaukaci ne?"
Munkiri: "Jirgin ruwa na itace wanda yake mataccen abu ne, ba shi da hankali ko rai, ta yaya zai dinga tafiya ba tare da matuki ko jagora ba?!"
Ali bin Maytham: "Shin maganata ce ta fi ban mamaki, ko taka da kake cewa wannan katon teku mai fadin gaske, yana tafiya ba tare da Mahalicci ko wani jagora mai hankali da rai ba!? Wadannan tsirrai iri-iri da suke fita daga kasa, da wannan ruwan sama da yake sauka daga sama, a tunaninka ba su da Mahalicci ko Mai tafiyar da su? Amma kuma kana mamakin yadda jirgin ruwa mai sauki zai yi tafiya ba tare da jagora ba!!"
Nan take wannan Munkirin Allah ya gaza bayar da amsa, ya cika da mamaki kuma kasa cewa komai. Ya gane cewa Ali bin Maytham ya kawo misalin jirgin ruwa ne domin ya ruguza dukkan hujjojinsa.
Madogara: Al-Fusus al-Mukhtar, na Sayyid Murtaza, Juzu'i na 1, Shafi na 31
Your Comment